Martanin Iran kan sabbin takunkuman EU
October 15, 2024Ministocin harkokin wajen kungiyar ta Tarayyar Turai ne dai suka yi taron duba wasu al'amuran suiyasa da yawa wadanda suka shafi Tarayyar ta Turai, inda taron da suka gudanar a kasar Luxembourg, ministoci su ka dauki matakin dora takunkumai kan kasar ta Iran kamar yadda Ursula von der Leyen, shugabar hukumar Tarayyar Turai ta fadawa manema labarai bayan taron, kan dalilansu na kara matsin lambawa Iran. Daga cikin sabbin takunkuman da Tarayyar Turai ta aza wa Iran dai harda hana wa wasu man'yan jami'an gwamnati yin tafiye-tafiye izuwa Turai. Seyed Hamzeh Ghalandari, mukaddashin ministan tsaron Iran yana cikin mutane bakwai da takunkumin na EU ya sanar da rike kadarorinsu da kuma hana su shiga kasashen Kungiyar ta EU. Haka kuma akwai kamfanonin jiragen saman daukar fasinjoji na Iran da Tarayyar Turai ta rike kadarorinsu, bisa laifin wai sune ke dakon kayan yaki da ake tallafawa Rasha da su.