1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Martani mai zafi kan kisan sojoji a Delta

March 18, 2024

Shugaba Bola Tinubu ya baiwa sojan Najeriya damar zakulo tsagerun da ake zargi da hallaka wasu sojoji 16 a kauyen Okuama na jihar Delta.

https://p.dw.com/p/4draH
Hoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Kama daga babban kwamandan askarawan tarayyar Najeriya ya zuwa ga kwamandoji na adawa ta siyasa da ma 'yan bokon da ke fadi ana sauraro dai, kisan sojojin Okuama ya zamo kafa ta hadewa wuri guda cikin kasar.

Kuma daukaci na bangarorin ba su boye ba bisa bukatar nemo 'yan laifin da daga dukkan alamu ke gudu irin na ceton ransu a halin yanzu. Takalar fada da kokarin cin fuska dai na zaman tuananin yan mulkin bisa abun da ya faru a kauyen Okuama da ke jihar Delta.

Bola Tinubu
Hoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Kuma a cewar kakakin fadar gwamnatin kasar Abdul Azeez Abdul Azeez shugaba Tinubun ya amince wa sojan yin duk mai yiwuwa a kokarin zakulo ‘yan laifin da nufin kaisu zuwa ga hukuncin da ke da zafin gaske.

Karin bayani: Sojojin Najeriya 16 sun kwanta dama a jihar Delta

Koma ya zuwa ina sojan ya ke shirin ya kai a kokarin cika burin na Abuja dai, rahotannin da ke fitowa daga yankin dai na nuna kona kauyuka da ma datse hanyoyi na rafuka a cikin farautar jiga jigan 'yan laifin.

Captain Abdullahi Bakoji dai na zaman wani tsohon jami'i a rundunar sojan Najeriyar da kuma ya ce yana kama da babban zunubi dauke rai na jami'in tsaron cikin batun zama na lafiya.

Taunin tsakuwa a kokari na aiken sako, ko kuma neman a wuce makadi cikin rawa mai dadi dai, Najeriya tana da tsohuwar al'adar mai da martani mai zafi bisa kisan sojoji a kasar. Kuma kama daga Zaki Biam zuwa kauyen Odi dai, fararen hular da ake zargi da kisan sun kare tare da dandanar bakar azaba.

Nigeria | Militärfahrzeug in Anambra | Archivbild
Hoto: Mosa'ab Elshamy/AP Photo/picture alliance

Karin bayani: Rikici tsakanin 'yan bindigar Niger Delta

To sai dai kuma kona kauyukan 'yan laifin a fadar Amnesty International ya saba da hankali da ma dokoki na kasar, acewar Isa Sunusi shugaba na kungiyar amnesty international da ke a tarayyar Najeriyar.

Duk da cewar dai suna da babban aikin kare iyakoki na kasar, sojan tarrayar Najeriyar dai na cikin jihohi sama da 30 da nufin kwantar da hankula cikin kasar dake fuskantar rigingimmu iri iri a halin yanzu.