Martani kan tara kudaden yakin neman zaben Jonathan
December 22, 2014Makudan kudadden da aka tara wa Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da sunan tallafawa ya janyo martani kan amfani da kudade a fagen siyasar kasar, da sannu a hankali ke zama zuba jari maimakon tsari na yi wa jama'a aiki domin ci-gaban kasa.
Domin kuwa fitattun ‘yan kasuwa da masu fada aji a kasar da karara a fili suka rinka ba da bilyoyin Naira da sunan gudumawar ga takarar ta Shugaba Jonathan ya sanya mayar da murtani bisa cewa ya fa sabawa dokar zabe ta Najeriyar. Shin menene illar yawaita amfani da kudi a kokarin neman kai wa ga madafan iko ga demokaradiyyar kasar? Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa ne da ke jami'ar Abuja.
"Babban hadarin wannan al'amari shine tuntuni muna ta kukan cewa siyasar Najeriya ta kasance ta kudi inda ake ta bushasha."
Abin da ya daukan hankali shi ne gudumawar da gwamnonin jam'iyyar PDP da ke mulki suka sanar da bayar ga wannan gidanauniya ta takarar Shugaba Jonathan, inda gwamnonin 21 suka ba da Naira milyan 50 kowanne a dai dai lokacin da jihohi da dama da jam'iyyar ke mulki suka gaza biyan albashi. Wannan ya sanya kungiyar kwadagon Najeriyar da ke fafutukar kare hakokin ma'aikata mayar da martani. Comrade Nasiru Kabir jigo ne a kungiyar kwadagon Najeriya, wanda ya nuna takaici da yadda ake jan kafa wajen biyan albashi a jihohin da jam'iyyar PDP ke mulki.
Sai dai ga jam'iyyar ta PDP na mai kare wannan mataki na ba da taimakon.
A yayin da ake ci gaba da kace-nace a kan wannan batu, a bayyane take amfani da kudi na yin mumunan tasiri ga harkar siyasar Najeriya duk da dakatar da bai wa jam'iyyu kudadde da hukumar zaben kasar ta yi a matsayin hanyar samun gyara.