Martani kan shari'ar 'yan Boko Haram
February 13, 2018Kotun ta yanke wa Haruna Yahaya mai shekaru 35 hukuncin zaman jarun na shekaru 15 bayan samunsa da laifin hada baki da kuma taimakawa wajen sace 'yan matan Sakandaren Chibok kusan shekaru hudu da suka gabata.
Haruna Yahaya ya amsa laifinsa kuma ya baiyana yadda suka je sakandaren Chibok suka kwashe 'yan matan da kuma rawar da ya taka yayin sace su da kuma wasu ayyukan kungiyar na hallaka mutanen da basu ji ba basu gani ba. Akwai kuma wasu mutane 19 wadanda su ma kotun ta same laifuka ta kuma yanke musu hukunci.
Wannan hukunci da aka yake wa mayakan na Boko Haram ya samu martani daga bangarorin dabam-dabam na rayuwa inda wasu suka yaba da abinda ya faru wasu kuma ke ganin hukuncin da aka yankewa Haruna Yahaya da ke da hannun wajen sace 'yan matan Chibok ya yi kadan.
Wasu daga cikin iyayen 'yan matan sun shaidawa sashen Hausa na DW cewa sun yi murna da hukuncin amma sun so a ce an matsa wajen gano wadanda suke sanya 'yan Boko Haraym din wannan danyen aikin.
Sai dai yayinda wasu ke ganin an yi sassauci a hukuncin wasu kuma na ganin hukuncin ya yi daidai.
A karon farko dai a wannan shari'a an baiwa manema labarai da kungiyoyin farar hula damar shiga domin sauraron shari'ar abinda ya sa kungiyoyin kare hakkin bil Adama yin marhabin da yadda ake shari'ar a yanzu.