Martani kan rahoton hukumar IAEA game da Iran
November 9, 2011Rahoton ya haddasa kace-nace a yankin gabas ta tsakiya, musamman tsakanin shugabannin Israila dake korafin cewar bai kamata a kyale kasa kamar Iran ta mallaki makamai na kare dangi ba.
Hukumar IAEA ta ambaci abin da ta kira, amintattun majiyoyi, wadanda tace sun nunarda irin ci gaban da kasar ta Iran ta samu a manufofin ta na kera makaman nuclear nuclear. Kasar Iran tasha nunar da cewar aiyukan ta na nuclear tana yin su ne saboda samarwa kanta makamashi, yayin da Israila da kawayen ta na yammja suke zargin cewar kasar burin ta shine ta kera makamai na kare dangi.
Iran tace rahoton na hukumar makamashi ta majalisar dinkin duniya bai kunshi wani abu sabo da duniyabata sans hi ba tuni. Jakadan kasar ta Iran a huikumar ta IAEA, Ali Asghar Soltanieh ya kwatanta wnanan rahoto a martsayin abu ne kawai na siyasa, wanda ya kera dokokin majalisar dinkin duniya, ya kuma raunana mutunci da darajar hukumar mai mazaunin ta a Vienna.
"Yace rahoton ba daidai bane, ba'a kluma tsara shi yadda ya kamata a yi shi ba: abune na siyasa, wadda aka rubuta shi karkashin matsin lamba daga Amerika. Tun daga shekarun da suka wuce, masu bincike akalla dubu hudu ne suka rika duba aiyukan da muke yi, wani lokaci ba tare da sun danar mana zasu zo ba, amma har yanzu basu sami wani abin fadi ba. Bamu da wnai abin boyewa. Duk aiyukan mu na nuclear muna yin su ne saboda makamashi. Haka ala'amarin yake. Babu wani abin da ya wuce aiyuka na zaman lafiya a Iran."
To sai dai rahoton hukumar ya tayar da hankali a yankin gabas ta tsakiya, musamman daga Israila, wadda tace wnanan rahoto ya kara fitar da take taken Iran a fili na samarwa kanta makaman nuclear. A baya-bayan nan an rika yada jita-jitan cewar Israila tana shirye-shiryen kaiwa tashoshin na Iran harin jiragen saman yaki domin lalata su, ko da shike kasashe da dama sun yi gargadin haka. Shi kansa shugaban Iran, Mahmud Ahmedinejad a wani jawabi ranar Talata a Teheran, yace kaiwa kasar Iran hari, daidai yace da cinnawa yankin gabas ta tsakiya gaba daya ta, wanda ita kanta Israila ba zata tsira daga gareshi ba. Iran, inji shi ba zata janye ko da taki daya ba daga manufofin ta, duk kuwa da barazanar gwada karfi kanta daga kasashen yamma. Shugaban jam'iyar adawa ta Israila, wato jam'iyar Labour, Zipi Livni tayi zargin cewar dari-dari da kasashen duniya suke yi da abin da Iran take aiwatarwa shine babban dalilin bata karfin gwiwar ci agaba da wannan shiri nata.
"Tace ya zuwa yanzu, mun lura da jan kafa daga wani bangare na kungiyoyi da kasashen duniya. A shawarwarin da nayi da shugabanin Rasha da na China, sun nuna cewar babu wnai abin da ya tabbatar da zargin da ake yiwa Iran, to amma yanzu an tabbatarda haka. Akwai fannoni da dama na takunkumi da har yanzuba'a fara aiwatar dasu ba, to amma yanzu suna iya yanke shawara kan makaman da za'a iya dauka kan Iran, ciki har da na diplomasiya da makamashi. Wajibi ne kuma ayi hakan cikin gaggawa, saboda a lokacin da muke ci gaba da dogon turanci, Iran tana ci gaba kan hanyar kera makaman nuclear."
Kasashen yamma kansu ya rarrabu a game da martanin da zasu mayar game da rahoton na hukumar IAEA. Kakakin ofishin harkokin waje na kungiyar hadin kan Turai, Maja Kocijancic tace rahoton yana da kanshin gaskiya a cikin sa, kuma ya kamata a dauki matakan kara tsananta takunkumi kan Iran. Shima kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amerika, yace wajibi ne kasashen yamma sun binciko amsar da ta dace a game dda manufofin Iran na samarwa kanta makaman nuclear. Yayin da Amerika take matsa lambar kara tsananta takunkumi kan Iran, kasashen Rasha da China, dukkanmin su masu ikon hawa kujerar naki a kwamitin sulhu, sun yi bayanin cewar kara matsa takunkumi kan kasar yana iya kawo cikas ga yiwuwar shawo kan matsalar ta hanyoyin diplomasiya.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita Usman Shehu Usman