Martani kan hana sanya Hijabi ko Nikabi
December 18, 2015A karshe taron da shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS suka gudanar a Abuja sun amince kan samar da doka ta hana amfani da hijibi da niqabi domin magance hare-haren da mata ke kaiwa cikin irin wannan shiga. Dama dai wasu kasashen Afirka sun fara haramta amfani da Niqabi, abinda shugabannin addini da ma kungiyoyin kare hakkin bani Adama ke dauka a matsayin tauyewa mutane hakkin yin shiga da addinin su ya tanadar.
Kungiyoyin addinai dai sun nemi shugabannin kasashen su lalubi hanyoyi na magance matsalar tsaro musamman ma dai batu na kai harin kunar bakin wake a wuraren taruwar jama'a maimakon hana mata amfani da hijabi wanda addini ya nemi matan su yi hakan. To sai dai duk da wannan, akwai masu ganin in har matakin zai haifar da samun zaman lafiya da kawo karshen hare-haren kunar bakin wake da mata ke kaiwa tsakanin al'umma suna goyon bayan wannan mataki.
Ana dai samun karuwar mata musamman ma masu kankantar shekaru da ke amfani da hijabi ko niqabi don kai harin kunar bakin wake tare da hallaka al'umma da dama inda ko a farkon makon nan wasu mata hudu sun yi yunkurin shiga birnin Maiduguri na jihar Borno don kai hare-hare amma jami'an tsaro suka dakile wannan yunkuri nasu, inda matan suka tada bam din da ke jikinsu kuma suka hallaka nan take.