Martani da yin Allah wadai da harin garin Kidal
March 9, 2015Da yake tsokaci kan wannan batu, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya ce kashe dakarun kiyaye zaman lafiya da ma fararan hula da aka yi a kasar ta Mali, abu ne da ba za a aminta da shi ba, kuma keta dokokin kasa da kasa ne na Bil-Adama. Daga nashi bangare Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya shi ma ya yi Allah wadai da harin, inda ya kara da cewa, tabas ne ko ba dade ko ba jima, wadanda suka aikata wannan aiki za su yi bayani a gaban kuliya.
Wannan hari da ya yi sanadiyyar rasuwar yara kanana biyu da soja daya dan kasar Chadi, na zuwa ne kwana daya kacal bayan wani harin da aka kai a birnin Bamako na kasar ta Mali, wanda ya yi sanadiyar rasuwar mutane biyar cikin su har da 'yan kasashen waje tare da jikkata wasu mutanen guda takwas. Sai dai har kawo yanzu babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin na Kidal.