1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilin Shugaban Koriya ta Arewa na Amirka

Zulaiha Abubakar
June 1, 2018

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya aika wani na hannun daman sa Kim Yong Chol da wasika zuwa ga shugaban kasar Amirka Donald Trump da yammacin Juma'ar nan inda tuni ma ya isa fadar mulkin Amirka ta White House.

https://p.dw.com/p/2yoxi
USA Mike Pompeo und Kim Yong Chol
Hoto: Reuters/M. Segar

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ne zai karbi bakuncin dan aiken daga Koriya ta Arewa kafin ya samu damar ganin Shugaba Donald Trump. Kasashen biyu dai sun jima suna nunawa juna  yatsa kan batun makamai masu linzamin da Koriya ta Arewa ta mallaka kuma ta ke yi wa duniya barazana da su.