Yuwuwar hadaka a siyasar Najeriya
January 12, 2023Tun daga daga jam'iyyar APC mai mulki da ma yar uwarta ta PDP da ke fatan komawa bisa mulkin dai hankali na tashe. Tsohuwar dabara dai daga duk alamu tana shirin karewa a bangaren jam'iyyun da a baya sukai kaurin suna a magudin zabe kuma ke kallon sauyi na fasahar da ke zaman ba sabun ba. To sai dai kuma manyan jam'iyyun sun yi nisa cikin zawarci na kananan jam'iyyu da ke shirin taka rawa da nufin kai wa zuwa ga kawancen da ke iya tasiri a tsakani na magoya baya.
A cikin jam'iyyu 18 da ke shirin taka rawa a zabukan kasar dai misali PDP ta adawa na fadin tana da kawance da 11 cikin fatan kwace madafun iko. A yayin da ita ma APC mai mulkin ke neman maimata dabarar da ta kai ta ga mulki wajen dorawa da kila kai lemar zuwa gidan tarihi.
Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu babu dalla-dalla bisa sabon tsarin na kawancen, akwai dai fatan goyon baya na kananan jam'iyyun na iya sauya fagen siyasar maras tabbas. A baya dai gamin gambizar jam'iyyun APC ta kai ga amfani kanta wajen cin mulkin a shekaru biyu baya. To sai dai kuma daga dukka na alamu ra'ayi na rabe a tsakani na kananan jam'iyyun da kusan dukkaninsu ke da masu takara har a mataki na shugaban kasar bisa hadewa wuri guda cikin suna na kawance. Ita ma jam'iyyar SDP tana tunanin turawa zuwa gaba, ga Accord Party da ke da fatan nasara a cikin zaben da ke tafe.
Duk da raunin rashin kudi da kila ma magoya baya dai kananan jam'iyyun sun yi kaurin sunan nuna amincewa da sakamakon zabukan kasar. Manyan jam'iyyu na kasar dai sun kafa tarihin amfani da kananan wajen karbe sakamakon zabukan cikin halin rudu da kila ma ba'a isa ba.