1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan hafsoshin tsaron Ecowas za su yi taro a Ghana

Binta Aliyu Zurmi
August 17, 2023

Hafsoshin tsaron ECOWAS za su yi wani taro a kasar Ghana, wanda ke da nufin sake duba dabarun na mayar da kasar a kan tafarkin mulkin dimukradiyya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

https://p.dw.com/p/4VGPs
Nigeria Abuja | ECOWAS-Treffen zur Lage in Niger
Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Taron na kwanaki biyu na zuwa ne bayan karuwar sabbin hare-haren ta'addanci da kasar ke fusakanta a baya-bayan nan, wanda rahotanni suka tabbatar da kisan sojoji sama da 17 da ke zama mafi muni tun bayan kifar da gwamnatin farar huula da suka zarga da yiwa tsaron kasar zagon kasa.

Kazalika ganawar ta manyan sojojin za ta kuma mayar da hankali a kan batun tura rundunar ko ta kwana a Nijar din, wanda a baya Ecowas ta jingine batun.

Sai dai masana na ganin wannan mataki da Ecowas ta maido da shi ka iya zama babbar matsala a bangaren sojin da ma siyasar kasar.

Karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afrika an yi zama na farko tsakanin kungiyar Ecowas da shugabannin sojin da ke rike da madafun iko a Nijar sai dai da alamu ba su kai ga cimma wata kwakwarar yarjejeniya ba.