Takaddamar Côte d'Ivoire da Mali
July 12, 2022Hukumomin kasar ta Mali dai na zargin dakaran wanzar da zaman lifiya ne na MINUSMA, duk da cewa ba su da takardar izinin gudanarda aiki mai kama da haka. Saidai rundunar wanzar da zaman lafiyar ta MINUSMA, ta bayyana cewa ba sojin ta ba ne. Tuni dai wannan batu, ya mamaye kafofin sada zumunta na zamani a Malin. Wasu kafofin yada labarai na kasar sun rawaito cewa a yayin da aka tsare jami'an na Côte d'Ivoire da ake zargi suna cikin rundunar ta MINUSMA filin jirgin sama na Bamako, ba sa sanye da kakin soja.
Kakakin rundunar ta MINUSMA Olivier Salgado ya bayyana a cikin shafinsa na Twitter cewa, sojojin da hukumomin kasar Mali suka tsare a Bamako a karshen wannan mako ba su da alaka da MINUSMA. Wasu 'yan kasar ta Mali, na bayyana da wani yunkurin juyin mulki da aka dakile a shafukansu sada zumunta. Wata majiya daga ofishin jakadancin kasar Côte d'Ivoire, ta nunar da cewa sojojin da a ka dakatar a Mali sun tafi aiki ne a ma'aikatar Sahelian Avition Service ta kasar Jamus a kan wata yarjajeniya da suka ratabawa hannu. Majiyar ta kara da cewa ba tsare su aka yi ba, an tura su makarantar horo ta jami'an Genderma kan wani jagoaranci na sojojin kasar ta Côte d'Ivoire.