1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali ta soke yarjejeniya da 'yan tawayen Abzinawa

January 26, 2024

Gwamnatin Sojin Mali ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar zaman lafiya na 2015, da aka kulla da 'Yan tawayen Abzinawa 'yan aware, don dakile ruruwar rikici da ka iya dagula al'amura a yankin na yammacin Afrika

https://p.dw.com/p/4bh4u
Kanal  Abdoulaye Maiga, mai magana da yawun sojin Mali
Kanal Abdoulaye Maiga, mai magana da yawun sojin Mali Hoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

kasar Mali dai ta sake tsintar kai cikin fargaba tun lokacin da sojin kasar suka hambarar da gwamnati a 2020 da 2021 da kuma kulla kawancen tsaro da sojojin hayan Rasha na Wagner tare kuma da korar sojojin Faransa da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar.

A wata sanar wa ta kafar talabijin gwamnatin sojin ta sanar da cewa babu wata yarjejeniya da 'Yan tawayen Abzinawa a halin yanzu, kasancewar sauran wadanda suka rattaba hannu a wancan lokacin sun ki cika alkawarin da suka dauka tare kuma da shakulatin bangaro da Algeriya ke yi a matsayinta na mai shiga tsakani.

Mali ta fada rikici tun a 2012 a loakcin da mayaka masu ikrarin jihadi da 'yan awaren Abzinawa, suka kaddamar da hare-hare a yankin sahara bisa zargin watsi da muradunsu da hukumomin Malin suka yi, inda suka bukaci kafa kasar su mai kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai ta Azwad.