Takaddama tsakanin Mali da MINUSMA
March 24, 2023Talla
Rahoton da hadakar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD MINUSMA ta wallafa a ranar Larabar da ta gabata ya nunar da cewa a shekarar 2022 an kashe mutane 1.277 sabanin shekarar 2021 inda aka kashe mutane 584 lamarin da ke nuna cewa an samu kari na kashi 54%, sannan kuma an samu laifin take hakin dan Adam sau 694 kuma kashi 35% daga ciki sojojin kasar ne tare da sabbin abokan huldarsu na kasashen ketare ke da alhakin aikatasu.
Yayin ta take martani kan rahoton ma'aikatar harkokin wajen Mali ta ce Majalisar Dinkin Duniya ba ta yi ba amfani da sahihan alkalumma wajen tattara bayanan kana kuma hakan ya isa ya kara dasa shakku kan labaran da majalisar ke bayar wa a kan kasar.