Ana tsamin dangantaka da Mali
July 15, 2022Matakin baya bayan nan da gwamnatin ta dauka na dakatar tsarin da Majalisar Dinkin Duniya ke tura sojoji na karba karba karkashin shirin jeka ka dawo don aikin wanzar da zaman lafiya ya sanya ayar tambaya akan yadda ta ke so da take so ta tsara sharudan gudanar da ayyukan, wani abin da manazarta suka ce yana iya tayar mata da balli.
Rundunar kiyaye zaman lafiyar ta MINUSMA a Mali wadda aka kafa karkashin kudirin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2100 a watan Afrilun 2013 tsawon shekaru yana kewayawa na jkarba karba inda ake tura sojoji na wani lokaci domin aikin tabbatar da zaman lafiya.
A yanzu gwamnatin mulkin sojin tana so ta kawo karshen wannan tsari bayan kama sojojin Ivory Coast 49 da suka sauka filin jirgin saman Bamako a wani jirgi na musamman a wannan makon.
Kasar Ivory Coast dai ta ce sojojin suna daga cikin kaso na biyar na dakarun MINUSMA da ta tura a tsarin jeka ka dawo da ake tura sojoji na karba karba, to sai dai gwamnatin sojin Malin ta baiyana su da cewa sojojin haya ne da suka shigo da wata manufa ta hambarar da gwamnatin.
Mataimakin kakakin Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq ya shaidawa yan jaridu a New York a jiya Alhamis cewa matakin na Mali zai haifar da mummunan sakamako ga sojojin da ke a kasar a yanzu da ke aikin kiyaye zaman lafiya.
Dakatar da aikin karba karbar zai shafi sojoji 12,261 da yan sanda 1,718 wadanda ke cikin ayarin rundunar kiyaye zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta tura zuwa kasar ta yammacin Afirka.
Wani masanin tsaro kuma daraktanbiyar nazari kan ta'addanci a yammacin Afirka Mukhtar Mumuni ya shaidawa DW cewa matakin shugabannin sojin Mali na dakatar da shirin karba karba na sojojin yana da matukar hadari.
"Idan manufar ita ce yanke hulda da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, da Faransa da kuma dukkan wadanda ke da dangantaka da Faransa to kuwa wannan mataki mummuna ne."
Ita ma gwamnatin Jamus ta mayar da martani inda mai magana da yawun ma'aikatar tsaro Arne Collatz ya yi bayani ga yan jarida yana mai cewa.
"Muna sane da cewa gwamnatin rikon kwarya a Mali ta sanar da MINUSMA cewa tana takaita ko dakatar da tsarin kewayen karba karba na tura sojoji. Dole ne Majalisar Dinkin Duniya ta tattauna da gwamnatin rikon kwaryar ta Mali domin a samar da wani yanayi da ya dace na aikin sojojin da ke kasa. Wannan ba Jamus kadai ya shafa ba. Sai an kammala wannan tattaunawa ne sannan za mu ce wani abu a game da makomar tura sojojin a Mali. Kafin nan duk wani abu da za a fada zai zama shaci fadi ne kawai."
Ita ma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Jamus Andrea Sasse tsokaci ta yi tana mai cewa.
"A kalamai na baka da gwamnatin Mali ta yi, ta tabbatar da cewa za su yi dukkan mai yiwuwa don ganin an cigaba da tsarin karba karba na sojojin ba tare da wani jinkiri ba. Babu shakka mun karbi abin da gwamnatin Malin ta fada, amma kamar yadda kuka sani mun sha baiyanawa karara muhimmancin da sojojin kiyaye zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya suke da shi ga a'ummar Mali wajen samun kwanciyar hankali a kasaar musamman yankin arewacin kasar da kuma kudirin mu akan wannan yana da matukar muhimmanci."
A halin da ake ciki dai Mali na fama da yan tada kayar masu ikrarin jihadi da suka bullo bayan boren Abzinawa a 2012 kuma sun yadu a kasashe makwabta inda suka kashe dubban jama'a da kuma tagaiyara wasu miliyoyin jama'ar a fadin yammacin Afirka na yankin Sahel.
Kawo yanzu dai sojojin Malin basu ce ga lokacin da za su gudanar da taro domin tattauna batun rundunar ta MINUSMA ba da ma kuma tsarin tura sojojin kiyaye zaman lafiyar na karba karba.