1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Minusma za su fice daga Mali

June 30, 2023

Kwamitin sulhu Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen aikin sojojin kiyaye zaman lafiya na Minusma a Mali daga wannan Jumma'a, kamar yadda gwamnatin mulkin sojan kasar ta bukata a tsakkiyar watan Yuni.

https://p.dw.com/p/4TI27
Ivorische Soldaten der UN-Friedensmission in Mali
Hoto: SIA KAMBOU/AFP

Sojojin na Mimusma su dubu 12 da ke jibge a Mali tun shekarar 2013 za su fice ga baki daya daga kasar cikin wa'adi na watanni shida mai farawa daga ranar ta 30 ga watan Yuni, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniyar ta sanar. 

Kuri'ar amincewa da bukatar ta Mali ta janye dakarun ta samu sahalewa daukacin kasashe 15 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun na MDD wanda ya yi zauma na musanman kan batun a wannan Jumma'a.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta tabbatar da cewa sojojin hayan Wagner za su ci gaba da aikinsu a Mali duk da yunkurin tawaye da shugaban kamfanin ya yi wa fadar Moscow a karshen makon jiya.