1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa fararen hula 600 kisan gilla a Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
March 24, 2022

Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren 'yan ta'adda da na kungiyoyin sa kai sun yi sanadin mutuwar fararen hula 600 a kasar Mali da ke fama da tashe-tashen hankula a shekarar 2021.

https://p.dw.com/p/48zGN
Sojojin Mali
Hoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/imago images

Wani rahoton da sashen kula da kare hakin bil Adama na rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Minusma ya fitar ya ce an samu karuwar kashe-kashen jama'a har da kaso 16 cikin dari a watanni shida na karshen shekarar da ta gabata a Mali, kana kuma kai tsaye rahoton ya nuna 'yar yatsa ga kungiyoyin sa kai da mayakan jihadi.

Rahoton na Munisma ya ce kungiyoyin jihadi kadai sun halaka kimanin mutune 206, baya ga wasu 239 da suka yi batan dabo daga watan Yulin shekarar bara zuwa Disamba, a yayin da su kuma kungiyoyin sa kai suka halaka mutun 70.

Ko baya ga kungiyoyin, rundunar ta kuma zargi dakarun sojan Mali da kisan fararen hulan da ba su san hawa ba su san sauka ba, zarge-zargen da gwamnatin kasar ta sha musantawa.