1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maleriya ta halaka mutane 4000 a Burundi

Yusuf Bala Nayaya
March 29, 2017

Sashin kula da huldodin jama'a a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa akwai mutane miliyan tara da suka harbu da rashin lafiya mai nasaba da maleriya a wannan kasa.

https://p.dw.com/p/2aG5w
ihi-2012: Probanden mit Malaria infizieren
Hoto: Sanaria Inc

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa cutar maleriya ta halaka mutane 4000 tun bayan da cutar ta bulla a kasar Burundi. Wannan adadi dai ya zamo na ban mamaki duba da cewa ministan harkokin lafiya a  kasar a ranar 13 ga watan nan na Maris ya ce mutane 700 ne suka rasu ta sanadin cutar ta maleriya a kasar ta Burundi.

Sashin kula da huldodin jama'a a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa akwai mutane miliyan tara da suka harbu da rashin lafiya mai nasaba da maleriya a wannan kasa da ke a Gabashin Afirka tun daga watan Janairu na shekarar 2016.

Akwai mutane miliyan 11 a wannan kasa ta Burundi da ta sake komawa rikici tun bayan hargitsin siyasa a shekarar 2015, ga matsala ta karancin abinci, abin da ya kara haifar da fargaba ta mutane da za su rasa rayuka. A cewar rahoton na Majalisar Dinkin Duniyar mutum guda cikin goma a Burundi na fama da kansa idan ana magana ta abincin da zai kai bakinsa.