Malala da Kailashi sun sami lambar yabo ta Nobel
October 10, 2014Ranar Juma'ar nan Kailash Satyarthi mai fafutukar yaki da bautar da kananan yara a kasar Indiya tare da yarinyar nan 'yar asalin kasar Pakistan mai fafutikar ganin an bar yara mata sun sami ilimin boko Malala Yousafzai ne aka karrama da lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya a shekarar 2014. Wannan yabo na su na zuwa ne duba da irin gudunmawar da su ke bayarwa wajen ganin yara sun sami makoma ta gari a rayuwarsu ba wai bautar da su ba.
Bautar da kanan yara a kasashen duniya na ci gaba da zama babban kalubale ga barazanar duniya musamman ganin yadda tashe-tashen hankula ke kara ruruwa a wasu sassa daban-daban na duniyar, wannan ne ya sanya wadanan zakuran mutane irinsu Kailash Satyarthi da ya sami horo a fannin injiniyan lantarki, a shekarar 1983 ya kafa wata cibiya da ake kira Bachpan Bachao Andolan (BBA), wacce ke fafutukar ganin bayan hana kananan yara ayyukan bauta , wacce tuni cikin ayyukanta ta sami nasarar kubutar da dubban yaran da ayyukan cin zarafin kananan yara.
Saura kadan Malala ta rasa ranta
Malala kuwa bayan tsira da ranta cikin fafutukar ta a wannan fage har yanzu ba ta sassauta ba, na baya bayannan ma a Najeriya sai da ta yi tattaki har kasar dan neman ganin shugaba Good Luck Jonathan ya yi duk me yiwuwa wajen ganin an sako yarannan 'yan makarantar Chibok. Irin wannan fafutuka ta kai gwarazan ga samun wannan lamba ta Nobel ta zaman lafiya kamar yadda Thorbjörn Jagland da yake magana amadadin kwamitin da ke bada lambar ke cewa.
"Kwamitin da ke bada wannan lambar yabon zaman lafiya ta Nobel na kasar Norway ya amince a wannan shekara ya bada wadannan lambobin girma ga Kailash Satyrthi da Malala Yousafzai saboda irin fafutukar su wajen ganin an kawo karshen gallazawa da bautar da kananan yara da matasado le yara su je makaranta da kuma ganin ba a take hakki ba ga kowane yaro ta hanyar bauta."
Wannan kwamiti me bada lambar ta Nobel ya duba muhimmancin da wadannan mutane da suka fito daga cikin addinan Hindu da Musulinci daga kasashen Indiya da Pakistan dan ci gaba da bada gudunmawarsu a fafutukar da ake wajen ganin an samar da ilimi da yaki da tsatstsauran ra'ayi. An gano cewa kimanin yara miliyan 168 ne ake bautar da su a yanzu a duniya, a shekarar 2000 kuwa a kwai karin wasu yaran miliyan 78 akan karin wannan adadi, wannan ke nuna irin nasarar da ake samu a wannan fafutuka.