1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Ana taro kan rikicin kasar

Ramatu Garba Baba
January 23, 2020

Kasashe da ke makwabtaka da Libiya sun shiga fafutukar ganin an magance rikicin da ke kokarin durkusar da kasar dama barazanar bazuwa zuwa sauran kasashen yankin.

https://p.dw.com/p/3WhQR
Libyen Feierlichkeiten 3. Jahrestag Revolution
Hoto: Reuters

Bayan wani Kudiri mai karfi da ya fito daga taron Berlin na kasar Jamus don sulhunta rikicin Libiya, a wannan Alhamis, wakilai na wasu kasashe da ke makwabtaka da Libiya ke wani zaman taro a Aljiyas babban birnin kasar Aljeriya don tattauna mafita kan rikicin da ke kokarin durkusar da kasar ta Libiya.

Taro ne na son ganin an cimma matsaya na dindin a tsakanin bangaren gwamnatin rikon kwaryar Libiyan da Janar Haftar da ke fada da juna, baya ga haka ministan harkokin cikin gidan Jamus Heiko Maas ya kasance daga cikin wadanda za su hallaci taron na wannan Alhamis, Mista Maas ya ce akwai bukatar a kara azama a kuma hada karfi da karfe in har ana son ganin bayan rikicin.

kasashen da suka shirya wannan zaman tattaunawar, sun hada da  Masar da Aljeriya da Tunisiya da Chadi da Sudan da kuma Mali. Libiya dai ta stunduma cikin rikici, bayan kisan shugaban kasar Mammar Ghadafi shekaru tara da suka gabata.