1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar mulkin Shugaba Jonathan

February 19, 2013

Rikicin siyasa a Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya da ƙaruwar rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan jam'iyyar na daɗa yin ƙamari.

https://p.dw.com/p/17hU0
Hoto: picture alliance / dpa

Sannu a hankali dai hadarin na ƙara baƙi da duhu. Kuma cikin kankanen lokaci yunwar ta kara kamari kuma hali na kowa na kara fitowa fili a gwagwarmayar neman ikon kasar ta Nigeria da ke kara fuskanatar sabon salon kuma ke neman kan gwara kan masu mulkin cikin jamiyyar PDP.

Babu dai zato ba kuma tsammani abun dahu ya bullo sarari a lokacin da aka wayi gari da daya daga cikin gwamnonin arewacin tarrayar Nigeria ya fito yana karatun ta kare ga shugaban kasar ga batun mulki a cikin kasar ta Nigeria

An dai ruwaito gwaman Babangida Aliyu na jihar Niger kuma shugaban gwamnoni na arewa yana karatun alkawarin da yace sun ƙulla da shugaba Jonathan na mulkin ƙasar sau ɗaya tilo. Alkawarin kuma da a cewar sa ke nufin adabo da sake takara ga shugaban a nan gaba. Abun kuma da ya harzuka fadar gwamantin ake zargin gwamna Aliyun da ƙoƙarin karya ga shugaba Jonathan

Ƙoƙarin cika alkawari ko kuma karatu irin na son zuciya dai tuni sabon rikicin ya kai ga rabon kai a tsakanin su kansu yayan jamiyyar PDP da rikicin ke barazanar rabawa ya zuwa gida gida.

Babban batu dai na tsakanin bin kaidar kundin tsarin mulkin kasar day a baiwwa shugaban wa'adi na shekaru takwas kan mulki abun kuma da a cewar Alhaji muhammed murtala dake zaman wani jigon jamiyyar a jihar Kaduna ke zaman mafita.

Wasa da hankalin yan Nigeria ko kuma rikici da suna na siyasa dai irin wannan cakulkulin ne ya kai ga PDP kai mulkin ta cikin kudancin ƙasar shekaru 13 da suka gabata amma kuma ke neman gaggarar sa dawowa a arewa a yanzu haka

To sai dai kuma a tunanin shehu musa gabam da shi kuma ke zaman jigon ta a Bauchi karatun na zaman na fifita ikon jamiyyar bisa biyan bukatar koma wanenen a cikin kasar

Wata jaridar kasar ta Nigeria mai zaman kanta dai ta Ambato wani taron da a cewar ta ya kai ga gudana a tsakanin gwamnonin jamiyyar 20 da kuma shugabaninta a cikin shekarar ta 2010 taron kuma da acikinsa ne ake batun sabon alkawri na shugaba Jonathan.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar