1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Majalisar Dokokin Girka

June 18, 2012

Zaɓen da ya baiwa jamiyyar masu ra'ayin mazan jiya nasara a Majalisa, ya bata damar girka haɗakar da ƙasar ke buƙata dan samar da hanyoyin tabbatar da ci-gaban ƙasa

https://p.dw.com/p/15Gwi
Leader of conservative New Democracy party Antonis Samaras is cheered by supporters after his statement on the election results in Athens June 17, 2012. Samaras claimed victory in Sunday's national election, saying Greeks had voted to stay in the euro single currency. REUTERS/John Kolesidis (GREECE - Tags: POLITICS ELECTIONS BUSINESS TPX IMAGES OF THE DAY)
Jagorar jamiyyar New Democracy Antonis SamarasHoto: Reuters

Hankulan 'yan al'ummar Girka sun fara kwantawa bayan zaɓen da aka gudanar, wanda ya baiwa jamiyyun da ke rajin karɓar tallafi daga ƙasashen Turai nasara a majalisar dokokin ƙasar. Jamiyyar masu ra'ayin mazan jiya ta New Democracy a ƙarƙashin jagorancin Antonis Samaras ta sami ƙuri'u kaɗan ƙasa da kashi 30, kuma jagorar yana neman girka haɗakar da ƙasar ke buƙata a Majalisar.

Jamiyyar Syriza mai adawa da matakan tsuke bakin aljihu ta amince ta sha kaye. Tun farko dai ta nemi a sauya wasu daga cikin sharuɗɗan da aka gindayawa Girkan na samun tallafi, abun da ya janyo fargabar cewa mai yiwuwa ƙasar ta bar rukunin ƙasashen da ke amfani da takardar kuɗin euro. To sai dai Samaras jagoran jamiyyar da ta yi nasara ya ce Girka ta zaɓi mutunta alƙawuran da ƙasar ta yi

"A yau mutanen Girka sun nuna amincewarsu da su cigaba da zama cikin Euro, su kuma kasance gaɓa mai mahimmanci tsakanin ƙasashe masu amfani da takardar kudin euro, su mutunta alƙawuran ƙasar su kuma tabbatar da bunƙasar tattalin arziƙi. Wannan nasara ta Turai ce baki ɗaya".

Samaras ya kuma bayyana aniyarsa na sauya wasu daga cikin sharuɗɗan matakan tsuke bakin alijihun amma ya ce mafi mahimmanci shine Girka ta cigaba da kasancewa a rukunin ƙasashen masu amfani da takardar kuɗin na bai ɗaya.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala