1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kiran taimakawa Yemen da tallafin kudi

December 18, 2011

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef yace ƙasar Yemen na dab da faɗawa yanayi makamancin na Somalia idan ba'a yi gaggawar tallafa mata da gudnmawar kuɗi ba.

https://p.dw.com/p/13VE1
A protestor chants slogans as he painted himself with Yemen's flag on his face and Arabic writing on his chest that reads "Be angry" during a demonstration demanding the prosecution of Yemen's President Ali Abdullah Saleh in Sanaa, Yemen, Wednesday, Nov. 16, 2011. (AP Photo/Hani Mohammed)
'Yan zanga zanga a Sanaa babban birnin ƙasar YemenHoto: AP

Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci samarwa ƙasar Yemen mai fama da rikici, tallafin kuɗi na gudunmawar jin ƙai Dala miliyan 450 domin ceto ƙasar daga abin da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta kira faɗawa yanayi irin na Somalia. Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu ƙungiyoyin agaji dake aiki a Yemen sun faɗawa wani taro da aka gudanar a Dubai cewa ƙasar Yemen na buƙatar taimakon jin ƙai musamman a fannin abinci da harkar kula da lafiya da tsabtar muhalli da kuma samar da ruwan sha mai tsabta. Zanga zangar adawa da shugaban ƙasar mai barin gado Ali Abdalla Saleh da aka shafe kusan shekara guda ana yi ta durƙusar da tattalin arzikin ƙasar lamarin da ya raunana matsanancin halin rayuwar Jama'a tare da ƙarancin abinci da ruwan sha da kuma wutar lantarki. Wakilin hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya Unicef Geert Cappalaere ya ce idan ba'a yi wani abu cikin gaggawa ba, to kuwa nan ba da jimawa ba za'a fuskanci babbar matsala a ƙasar.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman