Majalisar dokokin Rasha ta amice da wata doka
May 19, 2015Talla
Majalisar dokokin Rasha ta amince da wata doka wacce aka kwashe dogon lokaci ana yin ka ce na ce a kanta. Dokar dai za ta bai wa gwamnatin damar haramta kafuwar wasu ƙungiyoyin na ƙasashen waje a Rashar wanda gwamnatin ke ƙemarsu.
Majalisar ta amince da gaggarumin rinjaye da dokar a karatu na uku kafin a nan gaba shugaban Vladimir Putin ya rataɓa hannu a kan ta.