Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Isra'ila akan Falasdinawa
April 27, 2018Talla
Kwamishinan yayi wannan kira ne kafin Falasdinawan su fara zanga-zangar kashi na biyar a yau Juma'a a wani yunkuri na karya shingen da aka yi wa yankin su,ya kuma kara da cewar Isra'ila tayi watsi da gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mata bayan da ta yi amfani da makami mai guba akan fararen hula lamarin da yayi sanadiyyar rasa rayukan Falasdinawa 35 tare da jikkata sama da 1500 .