Amfani da masu neman mafaka a rikici
November 9, 2021Mai magana da yawun hukumar ta UNCHR Shabia Manto ta yi Alla wadai da amfani da mutanen da ke cikin matsin rayuwa domin cimma wata bukata ta siyasa.
Da take bayani ga Majalisar ta Dinkin Duniya, ta ce wannan ba shi ne karo na farko da ake amfani da bakin haure ko 'yan gudun hijira wajen takadammar da ke tsakanin kasashe ba, ta kara da cewar dole ne a gaggauta daina amfani da wadannan mutanen ta irin wannan hanyar.
Rikici tsakanin Belarus da kasashe mambobin kungiyar Tarayar Turai EU, ta yi tsami tun bayan da kungiyar ta kakabawa kasar wasu jerin takunkumai, a wani mataki na ramuwar gayya mahukuntan na Minsk sun bude iyakokinta da ya bai wa dimbin al'umma kwararowa.
Firaministan kasar Poland Mateusz Morawiecki ya ce tururuwar mutane da ke kokarin shiga kasarsa wani abin takaice ne da kuma barazana ga tsaro a daukacin kasashen Turai.