MDD ta tattauna kan rikicin Isra'ila
May 12, 2021Talla
Rashin cimma matsayar dai na zuwa ne bayan da Amirka da ke zama babbar kawar Isra'ilar ta nuna adawar hakan.
Amirka ta ce bata ganin cewa fitar da sanarwa zata iya yayyafa ruwa a wutar rikicin, sai dai kuma wakilai 14 cikin 15 na kwamittin sun yi amanar cewa sanarwar hadin gwiwa ka iya sassauta tashin hankali da ake ciki. Wakilin yankin gabas ta tsakiya na Majalisar Tor Wennesland ya yi gargadin cewa ta la'akari da yadda rikicin ke kara rincabewa, akwai fargabar rikicin ka iya sauya salo.
Ana dai ci gaba da lugudan wuta tsakanin bangarorin biyu, inda gomman mutane suka rasa rayukansu ciki har da yara a Gaza yayinda ita Isra'ila ta rasa wasu dakarunta.