1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mai da'awar jihadi ya kammalla zaman gidan yari

January 8, 2021

Abu Bakar Bashir da ke da alaka da harin bam da ya yi sandin rayukan mutane a Indonesiya ya kammalla zaman gidan kaso.

https://p.dw.com/p/3nh3M
Indonesien Haftentlassung radikaler Kleriker Abu Bakar Bashir
Hoto: ANWAR MUSTAFA/AFP

Malamin addinin nan da ke da alaka da kungiyar da'awar jihadi da kuma harin Bam da aka kai Bali na kasar Indonesiya Abu Bakar Bashir ya kammala zaman gidan kaso. Jami'an 'yan sanda sun baiyana cewa za su ci-gaba da sanya ido kan Abu Bakar Bashir wanda ya ke da shekaru 82 da haihuwa, yayin da dansa ya ce zai killace kansa a gida saboda annobar coronavirus. Bashir dan asalin kasar Yemen na daga cikin jagororin kungiyar Al-Qa'ida da ke da alhakin kai harin bam a shekarar 2002 a Bali na kasar Indonesiya da yayi sanandin rayukan mutum 202 wadanda da dama daga cikinsu masu yawon bude ido ne.