1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pyongyang na son ziyara daga jagoran Vatican

Yusuf Bala Nayaya
October 9, 2018

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya gayyaci Fafaroma Francis don ya kai masa ziyara, inda ya ce zai samu gagarumar tarba, kamar yadda shugaban kasar Koriya ta Kudu ya bayyana a wannan Talata.

https://p.dw.com/p/36F2J
Papst Franziskus besucht baltische Staaten
Hoto: Getty Images/AFP/T. Fabi

Shugaban kasar ta Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya kara da cewa zai isar da sakon na mahukuntan birnin Pyongyang zuwa fadar ta Vatican. Shugaban na Koriya ta Kudu dai zai kai ziyara fadar ta Vatican inda zai gana da fafaroma a ziyararsa da zai yi tsakanin 17 zuwa 18 ga watan nan na Oktoba.

Mai magana da yawun fadar ta Vatican Greg Burke ya ki cewa komai dangane da wannan batu ko ziyarar ta fafaroma zuwa Pyongyang sai dai ya bayyana a wannan Talata cewa a dan dakata tukuna wasikar ta mahukuntan Koriya ta Arewa ta karaso.