Mahawarar Turkiyya kan PKK
October 17, 2007A yau ne yan majalisar dokokin kasar turkiyya suka fara gudanar da mahawara adangane da kutsawa yankin arewacin Iraki da karfin soji,domin fatattakan tsirarun kurdawa yan adawa.
Duk da kiraye kirayen da kasahen duniya da kungiyoyi masu fada aji keyi kan wannan batu,turkiyyan na cigaba da daura aniyyanta na kutsawa cikin arewacin Irakin inda suke hada kan iyaka.
Shugabannin Turkiyyan dai sun jadadda cewar kaiwa yan adawan kurdawan harin soji ,dake jamiyyar maaikata kurdawan,wadanda ake kira PKK a takaice,bazai kasance cikin gaggawa koda majalisar ta amince da hakan ba.
Gabannin fara wannan mahawara ta yau a majalisar turkiyyan dai Prime ministan Iraki Nuri Al-maliki ,ya kira takwaransa na Turkiyyan ,inda ya bayyana cewar gwamnatinsa na muradin ganin cewar an kawo karshen ayyukan tarzoma da kungiyar ta PKK,ke aiwatarwa acikin kasar ta Iraki,tare da jaddada bukatar bangarorin biyu su cigaba da tuntubar juna.
A bangarensa sakatare general na mdd Ban Ki Moon yace taron kasa da kasa akan Iraki da Turkiyyan zata dauki nauyin gudanarwa a farkon watan Nuwamba zai taimaka wajen cimma matsaya guda tsakanin kasashen dake yankin kan wannan batu.
“Yace Gwamnatin Turkiyya zata zama mai masaukin baki na taron kasa da kasa akan halin da ake ciki a Iraki a farkon watan Nuwamba mai kamawa.Adangane da hakane na ke tabbatar dacewa, kowace daga cikin kasashen dake yankin,zatayi kokarin ganin cewar an tabbatar da zaman lafiya da tsaro a wannan yankin”
To sai dai duk dacewa prime ministan Iraki yace zasu cigaba da nazari dangane da hadin gwiwa da dakarun Turkiyyan,mataimakin shugaban kasar ta Iraki Tarek el-Haschemi,bayan ganawarsa da magabatan turkiyyana ya bayyana cewar.....
“Abun da nake hange bayan barina Iraki ,ya sabawa yadda aka tinkari lamarin,musamman adangane da halin da ake ciki acan.Don hakane nake ganin bukatar bada lokaci wa gwamnatin Irakin na amincewa hadin gwiwar dakaru da Turkiyya,domin maganta wannan matsalar ,wanda ayanzu yake cigaba da cin mutuncin harkokin tsaro na kasashen biyu.bawai ita Turkiyya kadai ba.Muma yana damun mu domin ya sabawa bkunduntsarin mulkinmu.”
To sai dai a bangaren Amurka tana ganin cewar afkawa kurdawan arewacin Irakin na PKk abangaren Turkiyya ita kadai ba shine mafita ba,kamar yadda kamakain maaikatar harkokin wajen Amurka Tom Cassey yayi nuni dashi..
“A tunani na babbar matsalarmu itace,daukan matakan soji a bangaren Turkiyya ita kadai ,ba shine mafita adangane da barazanar Jamiiyyar PKK ba”