1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya karbi bakoncin Putin a fadar Versaille

Mohammad Nasiru Awal SB
May 29, 2017

Ganawar shugabannin biyu na zama wani matakin bude sabon babi na huldar dangantaku tsakanin kasashen Faransa da Rasha.

https://p.dw.com/p/2dn7h
Frankreich - Paris - Vladimir Putin trifft Emmanuel Macron
Hoto: Getty Images/AFP/S. de Sakutin

Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron a wannan Litinin ya karbi bakoncin shugaban Rasha Vladimir Putin a fadar Versaille mai dadadden tarihi da ke a wajen birnin Paris, a wani abinda ke zama bude sabon babi na huldar dangantaku tsakanin kasashen biyu.

Macron ya yi alkawarin yin tattaunawa mai zafi a taronsa na farko da shugaban Rasha biyo bayan yakin neman zabe da tawagar Macron din ta zargi kafafan yada labarun Rasha da kokarin yi wa harkokin demokradiyyar Faransa kutse.

Macron wanda ya karbi ragamar shugabancin Faransa makonni biyu da suka gabata, ya ce tattaunawa da Rasha tana da muhimmanci wajen tinkarar jerin batutuwa da duniya ke takaddama kai. Duk da haka dangantakarsu na cike da rashin yarda inda gwamnatocin Paris da Mosko ke goyon bayan bangarori mabanbanta a yakin basasar kasar Siriya, kana suna kai ruwa rana kan rikicin Ukraine.