Shugaban kasar Faransa yayi kira ga Saudiyya
November 30, 2018Talla
Emmanuel Macron yayi wannan kira ne a yayin da shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya G20 ke gudanar da babban taronsu a kasar Ajentina a wannan Juma'ar.
Daga cikin shugabannin da suka halarci taron akwai wadanda suka soki lamirin matsayin Amirka kan zargin da ake wa kasar Saudiyya game da kisa da kuma batar da gawar 'dan Jarida Kashoggi.