Médecins sans frontières na matsin kaimi ga Amirka
December 10, 2015Talla
Wata takarda ce dai mai dauke da sanya hannu na mutane dubu 547 inda dukanninsu ke neman da a yi bincike na gaskiya kan harin da wani jirgin yakin kasar ta Amirka ya kai a wani babban asibintin kungiyar da ke birnin Kunduz na kasar Afghanistan.
Mutane kusan dubu dari biyar da hamsin, na kira ne ga shugaban na Amirka Barack Obama da ya aminta a aiwatar da bincike na kwakwab kan wannan lamari wanda kuma kwamitin kasa da kasa na agaji mai kula da bincike na musamman kan take hakin bil Adama na CIHEF zai gudanar da binciken. A daran 02 zuwa 03 ga watan Octoban bana ne dai da ya gabata, wani jirgin yakin kasar ta Amirka ya yi lugudan wuta a babban asibitin kungiyar da ke birbin Kunduz inda ya hallaka mutane 30.