London: Yemi Osinbajo ya gana da Shugaba Buhari
July 12, 2017Talla
Mai magana da yawun fadar mukaddashin shugaban na Najeriya ne Laolu Akande, ta shafinsa na Twitter ya sanar da ganawar tsakanin mukaddashin shugaban na Najeriya Yemi Osinbajo da Shugaba Muhammadu Buhari a birnin London. Sai dai kuma bai sanar da abubuwan da shugabannin biyu suka tattauna a kai ba.
Shugaba Buhari mai shekaru 74 da haihuwa ya bar kasar ta Najeriya tun ranar bakwai ga watan Mayu inda yake hutun jinya. Sai dai har kawo yanzu ba a sanar da takameman cutar da ke damunsa ba.
A watan Janairu da kuma Febrairu da suka gabata ma, shugaban na Najeriya ya shafe kimanin watanni biyu yana hutun jinya a birnin na London inda 'yan kasar Musulmai da Kiristoci suka yi ta yi masa addu'o'in samun lafiya.