Limaman Kirista sun saba wa yin tabarruki ga auren jinsi
December 28, 2023Limaman addinin Kirista a kasar Malawi sun bi sahun takwarorinsu a duniya da ke martani kan tsokacin da jagoran darikar Katholika Fafaroma Francis ya yi, na sahale wa limaman coci-cocin sanya wa masu auren jinsi albarka.
Wannan tsokaci na Fafaroma ya janyo zazzafar muhawara da kuma rarrabuwar kawuna a tsakanin wasu mabiya addinin Kirista a duniya, inda wasu ma suka shiga rudani.
Malawi dai na da mabiya darikar Katholika sama da miliyan biyu, wadanda kuma ke bibiyar al'amuran da ke wakana a fadar Vatikan sau-da-kafa. Wannan umarni na jagoran darikar ta Katholika Fafaroma Francis, ya janyo ra'ayoyi mabambanta a wannan kasa.
A yayin a ke ci gaba da ce-ce-ku-cen dai, shugaban wata kungiya mai rajin kare muradun al'umma a Malawi, Wonderful Mkutche ya shaida wa DW cewa babu ta yadda za a yi majami'un da suke da su, su tsallake umarnin fadar Vatikan, yana mai cewar akwai yiwuwar samun sauyi a nan gaba daga matsayar da ake bi a baya.
Father Valeriano Mtseka shi ne sakatare janar na majalisar limaman majami'un kasar Malawi bangaren mabiya darikar Katholika, ya bai wa mabiyan tabbacin cewa ba za su yi amfani da wannan umarni na fadar Vatikan ba.
A watan Yulin da ya gabata ne dai, limaman coci tare da wasu jagororin sauran addinai suka jagoranci wata zanga-zangar lumana a Malawi, da ke nuna kin amincewa da duk wata alaka da ta danganci auren jinsi a kasar.
Haka dai batun yake a Najeriya kamar wasu kasashen duniya, inda limaman majami'un suka barranta da tsarin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya rawaito. Mathis Sati daya ne daga cikin mabiya darikar, ya ce akwai damar kalubalantar umarnin.
A kasar Zambiya ma dai hukuncin daurin shekaru 15 ko ma na rai-da-rai ga aka ware wa masu auren jinsi, inda mabiya Katholikan suka nuna rashin gamsuwarsu da wannan umarni na Fafaroma. Haka ma a kasar Afirka ta Kudu, abin da ke gidan kaura dai shi ne ke a gidan goje.