Leftkowitz da Kobilka sun samu lambar yabo ta Nobel
October 10, 2012Talla
Wadannan masana biyu da ke bincike akan sinadirin protein da ke gina jiki an karrama su da wannan kyautar ne bisa gano wasu sinadirai daga jini da ke iya ba da bayanan yanayin jikin bil Adama. Makarantar Kimiya da ke a Stockohlm babban birnin Sweden ce ta ba da wannan sanarwa. Su dai wadannan sinadirai suna aiki ne wajen sarrafa hasken da ke cikin ido ko kuma tasirin da sinadirin Adrenalin ke yi akan kwayoyin jini. Akwai magungunan da dama da aka samar daga sakamakon bincike wadannan masana.
A ranar 10 ga watan Disamba, da ke zaman ranar tunawa da rasuwar Afred Nobel, wanda ya assasa wannan kyautar ne bukin ke kai kololuwarsa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu