1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Le Pen ta kai ziyarar ba-zata a Chadi

March 21, 2017

'Yar takarar jam'iyyar masu kyamar baki ta Faransa  a zaben shugaban kasa Marine Le Pen a ziyarar za ta gana da sojojin Faransa wadanda ke yin aikin kiyaye zaman lafiya a Chadi da ke a cikin rundunar Barkhane

https://p.dw.com/p/2ZdpD
Marine Le Pen
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Mori

Wannan ziyara dai 'yan siyasar kasar ta Chadi na yi ma ta kallon cewar daman wai a rina an saci zanen mahaukaciya, saboda kuwa tun da farko jagorar ta masu tsatsaurar ra'ayi na daga cikin wadanda suka amince da sake zaben da aka yiwa Idriss Deby Itno a matsayin shugaban kasa, a cikin watannin da suka gabata. Nasara da har yanzu 'yan adawar kasar ba su amince da ita ba, sannan kuma ga  siyasar da Marine Le Pen take yi ta nuna kyamar baki ita kan ta kadai wani abu ne da ya sa 'yan Afirka ke yi ma ta wani kallo. Laring Baou na daya daga cikin  membobin kwamitin gabatarwa na jam'iyyun adawa na kasar ta Chadi.

"Jam'iyyar masu Kyamar bakin na ganin cewar har kullum idan akwai matsala a Faransa to baki su ne dalilinta, hasalima 'yan Afirka wadanda suke yi wa kallon babban hatsari ga Faransa, bayan haka ko wa ya ga yadda ta yaba da zaben Idriss Deby. Zaben da dukkanin jama'a suka yi watsi da shi, ba mamaki gobe ta zo neman kudaden kampe wajen Deby, saboda ko wa ya san cewar 'yan siyasar Faransa shugabannin Afirka ne ke daukar nauyinsu.