Lauyoyin Nnamdi Kanu sun kalubalanci halarcin kotu
October 21, 2021Tun da karfe 10 na safe ne aka shigar da Nnamdi Kanu sanye da farar riga a kotun domin fara wannan shari'a, inda jami'an tsaro suka kakkare ko'ina. Sai dai bayan karanta masa laifuka guda bakwai da gwamnatin ke tuhumarsa da su, ya musanta cewa ya aikata laifukan. Jim kadan bayan wannan ne lauyoyin da ke kare shi Kanu suka shigar da kara suna kalubalanbtar laifukan da ma halarcin kotun na sauraran shari'ar domin laifi ne da ya aikata a London. Barrister Chukumeka Ejiofor wanda shi ne lauyan da ke kare shi ya ce don me za'a tuhume shi a Najeriya alhali a Birtaniya ya aikata laifin.
Jim kadan bayan da jami'an tsaro suka fice da Nnamdi Kanu daga kotu, 'ya'yan kungiyar Ipob suka danno suna rera takensu a gaban kotun suna nuna goyon bayansu ga Nnamdi Kanu, amma fa bayan da jami'an tsaro suka bar wajen.Dama dai an dai dauki matakan tsaro a wajen wannan shari'a domin duk wata hanyar da ta nufi kotun jami'an ‘yn sanda da sojoji sun tosheta, Hatta masu kokarin shiga don sauraron shari'ar da ma lauyoyinsun an hana su shiga, Babu ko da dan jarida guda da ya shiga kotun.
Lauyoyin da ke kare Nnamdi Kanu sun bukaci da a maida shi gidan yari maimakon ci gaba da ajiye shi a hannun hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS. Amma mai shari'a ta bayyana cewa saboda halin tsaro ne ake ci gaba da ajiye shi a wurin. An dage shari'ar har zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba domin ci gaba. Wannan ne karon farko da aka gabatar da Kanu a kotu tun bayan da aka kamo shi bayan da ya gudu daga belin da aka bashi. Wani wakilin ofishinb jakadancin Birtaniya ya hallarci shari'ar.
Wannan dai shari'a ce da ke daukar hankali a Najeriyar da ma kasashen waje wacce ke dalilin haifar da tashin-tashina musamman a yanki kudu maso gabashin Najeriya.