1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar yabo ta Nobel

December 10, 2006
https://p.dw.com/p/BuYU

Fitaccen masanin harkrkokin tattali daya samu lambar yabo ta Nobel,Muhammad Yunus,dayake karbar wannan lambar yabo ayau,yayi fatan cewa ,irin wannan sakayya zai taimaka wajen samarda hanyoyin yakar talauci a duniya.Mai shekaru 66 da haihuwa Mr Yunus,wanda ya sha bayyana maaikatan banki a matsayin mutane matalauta,ya karbi wannan lambar yabo ta Nobel ne da hadin gwiwan Bankinsa ta Grameen ,saboda tallafawa mutane marasa galihu,ta hanyar basu kananan rance.Daya jawabin bayyana godiyansa dangane da wannan lambar girmamawa daya samu,Mr Yunus ya bayyana cewa matsalolin tattali da na rayuwa ,da rashin ingantancen tsarin siyasa ,dana koma bayan muhalli da take hakkin biladama,na cigaba da barazana wa hartkokin zaman lafiya a duniya.Yunus wanda shine mutumin farko daya taba samun irin wannan lambar yabo daga kasar Bangladash,yace ana cigaba da samun karuwan talauci a duniya,saboda duniya taki taimakawa wadanda ya kamata a taimaka musu wajen yakar talauci.Bankinsa na Grameen dai,na mai zama bankin farko daya bawa talakawan Bangdash kudaden rance kanana,ba tare da laakari da matsayinsu ba,da kuma kaddarori da suka mallaka ba.