1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar yabo ta Nobel ta shekarar 2011

December 10, 2011

Wasu mashahuran mata guda ukku waɗanda suka nuna jamruntaka wajen samar da zaman lafiya a cikin ƙasashen su suka sami lambar yabon ta Nobel a bana.

https://p.dw.com/p/13QWs
Matan da suka samu lambar yabon, Leymah Gbowee a hagu, Tawakkul Karman a tsakiya da kuma Ellen Johnson-Sirleaf Shugabar Laberiya daga hannun damaHoto: dapd

Hukumar bada lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, ta ƙaddamar da bikin miƙa lambar Nobel ta shekarar bana ga wasu mashahuran mata guda ukku,a birnin Oslo na ƙasar Nowai.waɗanda suka haɗa da shugabar ƙasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf da wata mai fafutukar wanzar da zaman lafiya a Liberiya Leymah Gbowee,da kuma wata jagorar ci gaban dimokraɗiyya a Yemen Tawwakul Karman bisa jaruntakar da suka nuna na samar da zaman lafiya da ci gaba a cikin ƙasashen su.

Tawwakul Karman ta ce wannan kyauta na zaman ƙara hamzari ga yuyin juya halin da ake ci gaba da samun a cikin ƙasashen larabawa ''ta ce yaƙi ba faɗa ba ne kawai tsakanin gwamnatoci, ta ce a kwai wani yaƙi na shugabanni masu kashe al 'umomin su tare da cin amanar su. Sarkin Sweden Carl Gustaf na 16 shine ya miƙa sauran kyaututtukan ga mutanen da suka ci lambar yabo a fannonin daban daban waɗanda suka hada da na; tattalin arziki, da kiwon lafiya, da kimiyya da harhaɗa magunguna.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala