1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar yabo ta Nobel ga masana kimiyyar yanayin halitta

October 5, 2004

Masana kimiyyar Amurka guda uku ne aka zaba domin mika musu lambar yabo ta Nobel a sakamakon binciken yanayin halitta

https://p.dw.com/p/Bvfw

A lokacin da David Gross da David Politzer da kuma Frank Wilczek suka gabatar da sakamakon bincikensu na kimiyya a shekarar 1973, wanda daga bisani ya zama tushen wasu ayyukan binciken da suka biyo baya duka-duka shekarunsu bai wuce tsakanin 20 zuwa 30 da haifuwa ba. Wadannan matasa sun nuna karfin zuciya suna masu fatali da ikirarin magabatansu na cewar bata lokaci ne kawai, amma wannan aiki da suka sa a gaba ba ya da alfanu. Amma fa wadannan matasa ba su dadara ba suna masu nuna juriya da karfin hali na kutsa kai a tsakiyar wata mahaukaciyar guguwa domin binciko zahirin abin dake faruwa. A takaice Gross da Politzer da Wilczek sun taimaka wajen binciko wasu ‚yan kananan abubuwa na halittu, wadanda idan suka hadu bai daya suke da wani gagarumin tasiri. Bisa sabanin da yawa daga cikin takwarorinsu masana kimiyya, wadannan malaman guda uku sun ci gaba akan bincikonsu har sai da suka ga abin da ya ture wa buzu nadi. A lokacin da yake bayani a game da rawar da wadannan malaman kimiyya suka taka farfesa Lars Bergström cewa yayi:

Gungu daya na masana kimiyyar yanayin halittu suka rika tababa a game da yadda wasu ‚yan kananan abubuwa na halitta kan hadu su yi tasiri, kamar dai kwayoyin hada makamashin nukiliya. Amma godiya ta tabbata ga binciken da Gross da Politzer da Wilczek suka gudanar a yau an farga da abubuwa da dama kuma sakamakon binciken nasu na ci gaba da zama madogarar wasu matakan bincike da gwaje-gwaje na kimiyya.

Frank Wilczek na da shekaru 21 ne kacal lokacin da ya cimma nasarar matakin binciken da ya gabatar a hadin guiwa tare da malamansa Gross da Politzer. Tun daga wannan lokaci ya rika fatan samun lambar yabo ta Nobel ba tare da ya fid da kaunar cewa hakan zai tabbata watan-wata-rana ba. A saboda haka yake cikin doki da murna tun bayan da ya samu wannan labari na ba zata daga kwamitin lambar yabo ta Nobel da kuma taya murna daga gidan rediyon kasar Sweden.