1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar Yabo Ta Nobel Don Neman Zaman Lafiya

October 8, 2004

Wangari Maathai 'yar kasar Kenya ita ce ta samun lambar yabo ta Nobel don fafutukar neman zaman lafiya a bana sakamakon rawar da ta dade tana takawa wajen kare kewayen dan-Adam da daga matsayin mata a nahiyar Afurka

https://p.dw.com/p/Bvfn
Wangari Maathai
Wangari MaathaiHoto: AP

Mika wa Wangari Maathai wannan lambar yabo ta Nobel ta neman zaman lafiya, domin shiga jerin ‚ya’yan Afurka da suka samu lambobin yabo na Nobel, kamarsu Soyinka da Mandela da Gordimer, abu ne da ya kamata a yi madalla da shi. Tun da farkon fari ne aka sa ran cewar kwamitin lambar yabon ta Nobel zai mayar da hankali ne ga mata dangane da lambobin yabo na Nobel a game da rubutun adabi da kare hakkin dan-Adam da kuma fafutukar neman zaman lafiya, musamman ganin cewar in banda mace guda daya sauran wadanda suka samu lambobin yabo a fannin binciken kimiyya dukkansu maza ne. Ita dai Wangari Maathai ta cancanci samun wannan lamba ganin yadda tayi sama da shekaru 25 tana mai kutsa kanta a manufofin siyasa duk kuwa da hadarin dake tattare da lamarin. Shirin da ta gabatar a wajejen karshen shekarun 1970 bisa manufar dakatar da barazanar sare dazuzzuka a nahiyar Afurka ya zama zakaran gwaji ga manufofin dashen itatuwa da kare kewayen dan-Adam da kuma daga matsayin mata a duk fadin nahiyar. Duk da barazanar saka kafar wando daya da tsofon dan-kama-karyar kasar Kenya Daniel arap Moi da ta fuskanta, Wangari Maathai ba ta saduda ba tana mai shawo kan dalibai da malaman jami’a da talakawan yankunan karkara domin ba ta goyan baya ga manufarta ta kare makomar dazuzzukan Kenya. A matsayinta na malamar kimiyya, jami’ar tayi amfani da hazakar da Alla ya fuwace mata wajen hada kan manyan malamai da talakawan da ba su san ko bihim ba, kazalika da mawadata da matalauta karkashin laima daya kuma ta haka murnar shugaba Daniel arap Moi ta koma ciki dangane da matakan da ya rika dauka domin hana ruwa gudu ga wannan manufa. A cikin shekarun 1990 ta hada kan wani jerin gwanon da ya gudana a cikin ruwan sanyi a Nairobin Kenya domin bayyana adawa da wasu ‚yan baranda a tsakanin jami’an gwamnati dake fafutukar bannatar da wani gandon shakatawa na birnin domin gina gidajen haya. Hoton wannan zanga-zanga ya rutsa duk fadin duniya baki daya. Sau tari Wangari Maathai ta sha fama da raunuka sakamakon matakan muzantawa da mahukuntan Kenya ke dauka kanta, amma duk da haka ba ta ba da kai bori ya hau ga bukatun dan-kama-karya kuma tsofon shugaban kasar Daniel arap Moi ba. Wannan juriya da sadaukar da kai da tayi a fafutukar kare makomar kewayen dan-Adam a nahiyar Afurka shi ne mizanin da kwamitin lambar yabo ta Nobel yayi amfani da shi domin mika mata wannan lamba ta neman zaman lafiya.