Ko ya ta kaya a Olympics bana?
August 9, 2021A ranar Lahadin da ta gabata takwas ga watan Agustan da muke ciki, aka kawo karshen wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya Olympics a birnin Tokyo na kasar Japan. Wasannin da aka bude ranar 23 ga watan jiya na Yuli, a shekarar da ta gabata ya dace a yi su amma aka jinkirta sakamakon annobar cutar coronavirus da duniya ta fuskanta. Dangane da dalilin na corona, galibin wasannin an yi ba tare da 'yan kallo saboda bin matakan dakile yaduwar annobar.
Manyan kasashen duniya sun taka rawar gani sosai a wasannin Olympics na Tokyo. Kasar Amirka dai ta fi banbanta kanta tunda ita kadai ta kwashe zinari mafi yawa har guda 39, yayin da Chaina ke biye mata da zinari 38 sai kuma Japan mai masaukin baki da ta samu 27. 'Yan wasan Jamus sun koma gida ta filin jiragen saman birnin Frankfurt. Ita dai Jamus ta kare a matsayi na tara da lambobin zinare 10, azurfa 11 da tagulla 16. A nahiyar Afirka kasashen Masar da Tunisiya da Afirka ta Kudu duk sun samu lambar zinare yayin da Najeriya ta samu lambobi biyu na azurfa da tagulla kuma Najeriyar mafi yawan mutane a nahiyar ta Afirka ta kare a matsayi na 74.
A Lahadin karshen makon ne dai kuma, Lionel Messi shaharren dan wasan Ajantina ya yi bankwana da kungiyarsa ta Barcelona da ke Spain, inda ake sa ran zai koma kungiyar kwallon kafa ta PSG da ke kasar Faransa. Lokacin wannan bankwana gabanin jawabin da yayi, sai da Lionel Messi ya zubar da hawaye saboda yadda lamarin barin kungiyar ta Bacelona da ya kwashe tsawon rayuwarsa a fagen wasanni yana buga mata kwallo, ya sosa masa rai. Da yake jawabin nasa Messi cewa ya yi: "Ina matukar bakin ciki, saboda zan ban kungiyar, kungiyar da nake kyauna, a lokacin da ban yi tsammani ba."
Shi dai Lionel Messi ya ce lallai a shekarar da ta gabata ya yi yunkurin barin kungiyar ta Barcelona da ke Spain, amma haka ba ya cikin lissafinsa na wannan shekara.