1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barcelona ta lashe gasar La Ligar Spain

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
May 15, 2023

A daidai lokacin da Barcelona ta zama zakaran babban lig din Spain, ana taci-ba-taci ba tsakanin Bayern Munich da Dortmund a Bundesligan Jamus

https://p.dw.com/p/4RMpX
Bayern Munich ta lallasa Schalke da ci 6-0
Bayern Munich ta lallasa Schalke da ci 6-0Hoto: Adam Pretty/Getty Images

Bayan kare jini biri jini da aka yi ba tare da cin kwallo ba a wasanni biyu na kusa da na karshe na gasar Afirka ta 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa, Senegal ta kai banta ta bayan da ta doke Burkina Faso a bugun fenariti da ci 5-4. Ita kuwa Maroko ta fitar da Mali da ci 6-5 a wannan Lahadi 14 a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Kungiyoyin biyu wato Senegal da maroko za su fafata a ranar Jumma'a mai zuwa don kokarin lashe gasar AFCON U17 ta farko a tarihinsu, yayin da Burkina faso da Mali za su buga wasan sanin matsayi a ranar Alhamis mai zuwa.

An gudanar da wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka ta CAF. Kuma kamar yadda aka kyautata zato, Al Ahly ta Masar ta gasa wa Espérance Sportive de Tunis aya a hannu da ci 3-0, lamarin da zai sa ta tinkarar mataki na biyu na wasa cikin nitsuwa da kwanciyar hankali.

Yan wasan Kungiyar Al Ahly
Yan wasan Kungiyar Al AhlyHoto: Giuseppe Cacace/AFP

A nasu bangaren kuwa, Wydad Casablanca da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu sun yi canjaras, inda aka tashi wasan 0-0 duk da cewa tawagar Afirka ta Kudu ta yi wasa da 'yan kwallo goma sakamakon ba wa dan wasanta jan katin da alkalin wasa ya yi. 

A Najeriya kuwa, Kungiyoyin kwallon kafar kasar da suke fafatawa a gasar firimiya ta kakar 2022/2023 sun nuna kin amincewarsu game da ranar da kwamitin da ke lura da gasar ya IMC ya sanya domin barje gumi tsakanin manyan kungiyoyi shida da ake kira da Super Six kwanaki biyu kacal da kammala gasar firimiyar.  

Kungiyar FC Barcelona ta zama zakaran da Allah ya nufa da cara a babban lig din kwallon kafar kasar biyo bayan nasarar da ta yi da ci 4-2 a filin wasa na makwabciyarta Espanyol.  Wannan dai shi ne karo na 27 da  Barça ta samu kambun zakara a tarihin la Ligua.

Rabon Barcelona da kofin tun a 2019
Rabon Barcelona da kofin tun a 2019Hoto: Josep Lago/AFP/Getty Images

Dama rabon Barcelona ta zama zakara tun 2019 wato shekaru hudun da suka gabata. Dadin dadawa kuma wannan shi ne babban kofi ko matsayi na farko da Xavi ya lashe, wato tsohon dan wasan Barça wanda ya karbi ragamar horar da kungiyar shekaru biyun da suka gabata, amma ya lashe gasar kofin kalubale na Spain guda daya kacal.

A Jamus kuwa, har yanzu ba a san matsayi tuwo ba tsakanin Bayern Munich da Borussia Dortmund sakamakon nasara da suka yi a mako na 32 na Bundesliga. Ita dai yaya-babba ta yi wa Schalke 04 dukan kawo wuka 6-0 a a filin wasa na Allianz Arena, kuma ta gudanar da wasa mafi kyawu tun bayan zuwan koci Thomas Tuchel a watan Maris da ya gabata. Wannan nasara ta uku a jere da Bayern Munich ta yi a gasar Bundesliga, ya sa mafarkin ci gaba da rike kambun zakara da ke hanunta, amma Borussia Dortmund na ci gaba da cin dunduniyarta, inda maki daya ne kacal ke tsakaninsu a daidai lokacin da ya rage a makonni biyu a nade tabarmar Bundesliga. 

Sai dai kamar yadda ake tserereniyar darewa saman teburin Bundesliga, haka lamarin yake a kasa inda har yanzu ake tserereniyar zama cikin dangi wato baaban lig din kwallon kafar Jamus. A wannan rukunin, Bochum ce kadai ta cire wa kanta kitse a wuta sakamakon doke Augsburg da ta yi da ci 3-2 don haka ta fito daga rukunin 'yan baya ga dangi, kuma ta koma matsayi na 15. Amma dai Stuttgart, wacce ta yi 1-1 da Bayer Leverkusen tana a matsayi na 17, yayin da Hertha Berlin da ke cikin yanayi mafi rikitarwa ta sha dima ci 5-2 a hannun Köln, za ta buga wasanta na warewa ko warwarewa da VfL Bochum. 

Novak Djokovic
Novak DjokovicHoto: Pavel Mikheyev/REUTERS

Fitaccen dan wasan tennis na duniya Novak Djokovic ya yi nasara a wasanni biyu a jere a karon farko a bana don samun tikitin zuwa mataki na gaba na Masters 1000 a Rome na Italiya. Dama dai yana kare kofin da ke hannunsu, wanda ya lashe sau bakwai, amma ya fuskanci kalubale kafin ya doke dan Bulgariya Grigor Dimitrov mai matsayi na 33 a duniya da ci 6-3, 4-6, 6 - 1

A gasar ta Rome dai, dan asalin Italiya Jannik Sinner (N.8) shi ma ya samu tikitinsa zuwa wasa na gaba  bayan doke Alexander Shevchenko na Rasha da gumin goshi da ci 6-3, 6-7 (4/7), 6-2. Shi kuwa Stefanos Ttispas (N.5), cikin sauki ne ya kammala wasan da ya yi da dan Portugal Nuno Borges da ci 6-3, 4-3. Yayin da Bajamushe Alexander Zverev (N.19), wanda ya samu nasara a gasar Roma a 2017, ya shafe kusan 2h30 kafin ya yi waje road da dan Beljiyam David Goffin da ci 5-7, 6-3, 6- 4. A nasa bangaren  Daniil Medvedev dan Rasha ya ba wa mara da kunya ta hanyar lashe wasansa na farko a Roma, inda ya yi fatali da Finn Emil Ruusuvuori da ci 6-4, 6-2.