1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni

Suleiman Babayo LMJ
March 15, 2021

Martani game da zaben shugabannin Hukumar Kula da Wasan Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka da tarnakin da annobar cutar coronavirus ta haifar a bangaren Cricket a kasashen da suka yi fice a wasan.

https://p.dw.com/p/3qewj
Fußbal | Caf - Dr Patrice Motsepe
Sabon shugaban Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka CAF, Patrice Motsepe Hoto: Muzi Ntombela/BackpagePix/empics/picture alliance

Mai arziki dan Afirka ta Kudu, Patrice Motsepe wanda ya kasance dan takara daya tilo a yayin zaben na shugaban Hukumar Kula da Wasan Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka, yayin zaben da aka gudanar a ranar Jumma'ar da ta gabata a birnin Rabat na Moroko.

Kasar Ostreliya tana cikin kasashen duniya suka yi fice a fagen wasan Cricket, sai dai samun bullar annobar cutar coronavirus ya shafi wasan kamar sauran fannoni wasanni.
A wasannin lig na Jamus da ake kira Bundesliga da aka fafata a karshen mako kuwa, Augsburg ta samu nasara a kan Borussia Mönchengladbach da ci uku da daya. Wolfsburg ta bai wa Schalke 04 kashi da ci biyar da nema. Union Berlin kuwa ta lallasa Cologne ne da ci biyu da daya, yayin da Mainz ta bai wa Freiburg kashi da ci daya mai ban haushi. Ita ma dai Dortmund a wannan makon ta yi abin kai, inda ta yi nasara a kan Hertha Berlin da ci biyu da nema.

FC Augsburg v Borussia Moenchengladbach - Bundesliga
Fafatawar da aka yi tsakanin Borussia Mönchengladbach a karshen makoHoto: Matthias Balk/dpa/picture alliance