Labarin Wasanni: 02.11.2020
November 2, 2020Masu sauraro barkanmu da saduwa a cikin shirin na Labarin Wasanni inda za mu duba ci gaba da wasannin lig-lig na kasashen Turai, inda hukumomi a Jamus suka sake daukar matakin hana takaitattun 'yan kallon shiga filayen wasa saboda tsoron sake yaduwar annobar coronavirus. Kana shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Afirka, Ahmad Ahmad ya bayyana shirin sake takara a zaben shekara mai zuwa domin samun wa'adi na biyu da kuma wasu fannonin wasannin.
Za mu dauko shirin da wasan lig na Jamus da ake kira Bundesliga inda a karshen mako kungiyar Bayern Munich ta bi FC Kolon har gida ta fita iya rawa da ci biyu da daya. Augsburg ta ci Mainz da ci 3 da 1.
Daga nan Sashen Hausa na DW mun gabatar da wasa tsakanin Arminia Bielefeld wadda ta gaza jefa kwallo a gida Borussia Dortmund inda Dortmund ta doke ta da biyu da nema.
An dai sake mayar da wasannin lig na Jamus na Bundesliga karkashin matakan yaki da annobar corona, kuma a cewa shugaban hukumar wasan kwallon kafar kasar, Fritz Keller ya nemi kwantar da hankali domin kasadar kamuwa da cutar yayin buga kwallon kalilan ne.
Bude takarar neman shugabancin Hukumar CAF
Shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa na nahiyar CAF, Ahmad Ahmad ya sake tsayawa takara a shekara mai zuwa domin neman sabon wa'adi na biyu na jagorancin wannan hukuma. Ahmad Ahmad da hukumarsa sun fuskanci matsaloli da tarnaki yayin wannan wa'adi da suka hada da ladaftarwa daga hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya, FIFA. Zuwa ranar 12 ga wannan wata na Nowamba ake rufe karbar sunan 'yan takara a hukumar mai kasashen 54 a matsayin wakilai. Kawo yanzu daga cikin wadanda suka nuna sha'awar takara akwai Tarek Bouchamaoui daga kasar Tuniya wanda yake cikin kwamitin zartaswa ta hukumar ta CAF da hukumar FIFA, amma kawo yanzu bai samu goyon bayan da ake bukata na takara ba tukunna. Tuni dai Ahmad Ahmad ya samu goyon bayan shugabannin hukumar kwallon kafa na kasashen 46 daga cikin 54 mambobin hukumar.