1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyandar biri ta bulla a Kwango

April 24, 2024

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango sun ce mutane 19 sun kamu da cutar kyandar biri a kasar.

https://p.dw.com/p/4f8nZ
Kyandar biri ta bulla a Kwango
Kyandar biri ta bulla a KwangoHoto: Isai Hernandez/imago images

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango sun tabbatar da bullar cutar kyandar biri a kasar ciki har da babban birnin kasar, Brazzaville. Ministan kiwon lafiya na kasar, Gilbert Mokoki ya ce an samu rahotanni mutum 19 da suka kamu da cutar.

Mista Mokoki ya ja hankalin jama'ar kasar da su dauki matakan dakile yaduwar cutar ta hanyar kaucewa cudanya da wadanda suka kamu da ita da kuma wasu dabobbi da ma kaucewa ta'amulli da danyen naman dabobbin dawa.

Karin bayani: Najeriya: Gomman mutane sun kamu da kyandar biri

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa alamomin cutar sun hada da zazzabi da guraje da kuma marurai. A shekarar 1970 ne dai aka faro gano cutar ta kyandar biri a jikin dan Adam a kusa da Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango a cewar Hukumar lafiya ta duniya WHO.