Kwamitin sulhu ya gargadi 'yan Houthi
February 16, 2015Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci 'yan Shi'an Houthi da suka karbe mulki a kasar Yemen da su sauka idan suna son kansu da lafiya. Sannan kuma ya yi barazanar gurfanar da su 'yan bindigan da ke da goyon bayan Iran gaban kuliya, idan ba su kawo karshen rikicin siyasa da suke haddasawa a kasar ta Yemen ba.
Mambobin kwamitin 15 sun kuma yi kira ga kasashen waje da su daina yin shisshiga a harkokin cikin gidan Yemen, da take fama da rikici tun bayan da guguwar neman sauyi ta kada shekaru hudu ke nan da suka gabata.
Mayakan Houthi sun mayar da Sana'a babban birnin karkasghin ikonsu tun watan Satumban da ya gabata tare da kakkange madafun iko. Hakazalika mabiya mazhabar ta shi'a sun rusa gwamanti da kuma majalisa tare da yi wa shugaban da ya yi murabus daurin talala.
Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a karashen mako don yin Allah wadai da salon mulki na 'yan Houthi.