Kungiyoyi sun fice daga hukumar zabe a Chadi
April 1, 2016Kungiyoyn fararen hula da na kwadago a kasar Chadi sun janye wakillain daga hukumar zaben kasar ta CENI tare da jaddada ranar biyar ga wannan wata na Afrilu matsayin ranar da za su yi babban jerin gwano na lumana wadda ba a taba yin irinta ba a cewar gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar cikin wata sanarwa a wannan Jumma'a.
Yayin da yake karanta sanarwar, mataimakin sakatare janar na kungiyar gwadagon kasar ta Chadi ta UST, Goukouni Vaima, ya ce bisa la'akari da yadda har yanzu ake tsare da abokansu shugabannin wasu kungiyoyin fararen hula guda hudu a gidan kaso kimanin kwanaki 10, sun dauki aniya daga bakin wannan rana ta Jumma'a ta janye duk wakillansu daga tsarin harkokin zaben kasar ta Chadi wanda zai gudana a ranar 10 ga wannan wata na Afrilu.