Nijar: An koka da zaftare kudaden harajin ma'adinai
June 27, 2018A wata 'yar gajeruwar sanawar da hadin gwiwar kungiyoyin mai akalla shafi biyu suka fitar, kungiyoyin na farar hula sun yi tir da Allah wadai game da matakin da hukumomin kolin Jamhuriyar ta Nijar suka dauka a ya yin wani taron majalisar ministoci na makon jiya wanda sanarwar karshen taron ta tabbatar da zaftare harajin TV ga wasu kamfanoni masu hakar ma'adanu da suka jima suna aikin hako dimbin tattalin arzikin Nijar a yankuna daban daban ko kuwa ma sababin da suka soma aikin ta hanyar kawo gyaran fuska ga dokar hako ma'adanan da gwamnatin ta rattabawa hannu tun a shekarar 1993.
Duk da dimbin tattalin arzikin da Allah ya huwacewa Nijar dai bai kai ga samun wadatar tattalin arzikin ba ga jama'a inji kungiyoyin, wanda galibi a yankunan da ake hako ma'adanun talakawan ke kasancewa a cikin mawuyacin hali wanda hatta ma ga gwamnatin inji 'yan kungiyoyin ma'adanan na karkashin kasa, abinda suke sanyawa a cikin aljihun gwamnatin bai taka kara ya karya ba, kana a cikin wannan yanayi ne gwamnatin ta yi kukan kura domin ta tarbi aradu da ka.
Kungiyoyin dai sun ce dole fa a yanzu gwamnatin ta farga duba da matsin lanba na tattalin arzikin da ta ke fuskanta domin kuwa bincike na kungiyoyin ya nuna cewar gwamnatin na dimbin hasara Inji Malam Aissami Mahamadou Tchiroma kakakin kungiyoyin.