1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Hamas ta sha alwashin kare yankin ta

Ramatu Garba Baba
August 10, 2020

Kungiyar Hamas ta ce, za ta ci gaba da kare yankinta daga duk wata barazana daga Isra'ila bayan da ta kai wani hari da rokoki a yankin tekun Mediterranean da ke karkashin ikon Isra'ilan.

https://p.dw.com/p/3gjdc
Israel Gaza l  Raketenangriffe l Gaza-City Rauch nach Luftangriffen aus Israel
Hoto: Getty Images/AFP/M. Abed

Kungiyar da ke rajin kare hakkin Falisdinawa ta Hamas ta kai hari da rokoki kan yankin Isra'ila a wannan Litinin. Wani mai kusanci da kungiyar ta Hamas, ya ce harin, tunatarwa ce ga Isra'ilan, cewa a shirye Hamas ta ke ta kare kanta, don kuwa, ba zata nade hannunwanta ba a yayin da ta ke ci gaba da fuskantar barazana daga Isra'ilan.

Rokoki dai kimanin takwas aka gani an harba zuwa yankin tekun Mediterranean da ke karkashin ikon Isra'ilan. Rikicin dai baya rasa nasaba da kara yawan dakarunta da Isra'ilan ta yi a kan iyakarta da yankin Zirin Gazan na Falasdinu.